Acts 19

Bulus a Afisa

1Lokacin da Afollos yake a Korinti, Bulus ya bi hanyar da ta ratsa ta Asiya ya zo Afisa. A can ya sadu da waɗansu almajirai, 2sai ya tambaye, su ya ce, “Kun karɓi Ruhu Mai Tsarki saʼad da kuka gaskata?”

Suka amsa suka ce, “Aʼa, ba mu ma san akwai Ruhu Mai Tsarki ba.”

3Saboda haka Bulus ya yi tambaya, ya ce, “To, wace baftisma aka yi muku?”

Suka ce, “Baftismar Yohanna.”

4Bulus ya ce, “Ai, baftismar Yohanna, baftisma ce ta tuba. Ya faɗa wa mutane su gaskata a wani wanda yake zuwa bayansa, wato, Yesu.” 5Da ji wannan, sai aka yi musu baftisma a cikin sunan Ubangiji Yesu. 6Da Bulus ya ɗibiya musu hannuwansa, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauka musu, suka kuwa yi magana da harsuna, suka kuma yi annabci. 7Mutane kuwa su wajen mutum goma sha biyu ne.

8Bulus ya shiga majamiʼa ya yi magana gabagaɗi a can na watanni uku, yana muhawwara yana kuma rinjayarsu game da mulkin Allah. 9Amma waɗansunsu suka taurara; suka ƙi su gaskata kuma a gaban jamaʼa suka yi baƙar magana game da Hanyar. Bulus kuwa ya bar su. Ya tafi tare da almajirai ya dinga tattaunawa da su kullum a babban ɗakin jawabi na Tirannus. 10Wannan ya ci gaba har shekara biyu, sai da dukan ya sa dukan Yahudawa da Helenawa da suke zaune a lardin Asiya suka ji maganar Ubangiji.

11Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus, 12har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su.

13Waɗansu Yahudawa masu yawo gari gari suna fitar da mugayen ruhohi suka yi ƙoƙari su yi amfani da sunan Ubangiji Yesu a kan waɗanda suke da aljanu. Suna cewa, “A cikin sunan Yesu wanda Bulus yake waʼazi, na umarce ku, ku fito.” 14ʼYaʼya bakwai maza na Sikeba, wani babban firist na Yahudawa, suna yin haka. 15Wata rana mugun ruhu ya amsa musu ya ce, “Yesu kam na sani, Bulus kuma na sani, amma ku kuma su wane ne?” 16Sai mutumin da yake da mugun ruhun ya fāɗa musu ya sha ƙarfinsu duka. Ya yi musu dūkan tsiya har suka fita a guje daga gidan tsirara jini yana zuba.

17Da Yahudawa da Helenawan da suke zama a Afisa suka ji wannan labari sai duk tsoro ya kama su, aka kuwa darjanta sunan Ubangiji Yesu ƙwarai. 18Da yawa cikin waɗanda suka gaskata yanzu suka zo a fili suka furta mugayen ayyukansu. 19Waɗansu masu yin sihiri suka kawo naɗaɗɗun littattafansu wuri ɗaya suka kuwa ƙone su a gaban jamaʼa. Saʼad da aka lissafta yawan kuɗin naɗaɗɗun littattafan nan, sai jimilar ta kai darakmas dubu hamsin. 20Ta haka maganar Ubangiji ta bazu koʼina ta kuma yi ƙarfi.

21Bayan dukan wannan ya faru, sai Bulus ya yanke shawara ya ratsa Makidoniya da Akayya in za shi Urushalima. Ya kuma ce, “Bayan na tafi can, dole in ziyarci Roma ita ma.” 22Sai ya aiki biyu daga cikin masu taimakonsa, Timoti da Erastus, zuwa Makidoniya, yayinda shi kuwa ya ɗan dakata a lardin Asiya.

Hargitsi a Afisa

23Kusan wannan lokaci sai aka yi wani babban hargitsi game da wannan Hanyar. 24Wani maƙerin azurfa, mai suna Demetiriyus wanda yake ƙera siffar ɗakunan tsafin Artemis da azurfa, ba ƙaramin ciniki yake kawo wa mutane masu sanaʼar nan ba. 25Sai ya tara su wuri ɗaya, tare da masu irin wannan sanaʼar, ya ce, “Ku jamaʼa, kun san muna samun kuɗin shiga sosai daga wannan sanaʼa. 26Kuma kuna ji kuna gani yadda Bulus ɗin nan ya shawo kan mutane da yawa ya kuma sa suka bauɗe a nan a Afisa da dukan lardin Asiya. Yana cewa alloli da mutum ya ƙera ba alloli ba ne ko kaɗan. 27Akwai hatsari, ba kawai cewa sanaʼarmu za ta rasa sunanta mai daraja ba, amma za a yi banza da ɗakin tsafin Artemis alliyarmu mai girma, alliyar kanta wadda ake bauta a koʼina a yankin Asiya da kuma duniya, za a raba ta da darajarta.”

28Da suka ji haka, sai suka yi fushi ƙwarai suka fara ihu suna cewa: “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!” 29Jim kaɗan sai hayaniya ta tashi a dukan birnin. Sai mutane suka cafke Gayus da Aristarkus, abokan tafiyar Bulus daga Makidoniya, suka ruga da zuwa fili da nufi ɗaya. 30Bulus ya so ya bayyana a gaban taron, amma almajirai ba su bar shi ba. 31Har waɗansu shugabannin lardin ma, abokan Bulus, suka aika masa suna roƙonsa kada ya kuskura ya shiga filin nan.

32Taron kuwa ya ruɗe: Waɗansu suna ihu suna ce abu kaza, waɗansu kuma wani abu dabam. Yawancin mutane kuma ba su ma san abin da ya sa suke a wurin ba. 33Yahudawa suka tura Alekzanda gaba, sai waɗansu a taron suka riƙa yin masa ihu. Sai ya ɗaga hannu don a yi shiru don yǎ kāre kansa a gaban mutane. 34Amma saʼad da suka gane shi Bayahude ne, sai duk suka yi ihu gaba ɗaya na kusa saʼa biyu, suna cewa, “Girma ta tabbata ga Artemis ta Afisawa!”

35Sai magatakardar birnin ya sa taron su yi shiru, saʼan nan ya ce, “Mutanen Afisa, ashe duk duniya ba ta san cewa birnin Afisa ce mai lura da haikalin Artemis mai girma da kuma siffarta da ya fāɗi daga sama ba? 36Saboda haka, da yake ba dama a yi mūsun wannan gaskiya, ya kamata ku natsu kada ku yi kome da garaje. 37Kun kawo mutanen nan a nan, gashi kuwa ba su yi fashin haikali ba, ba su kuwa saɓa wa alliyarmu ba. 38To, in haka ne, in Demetiriyus da abokan sanaʼarsa suna da wata magana game da wani ai, kotuna suna nan a buɗe, akwai kuma muƙaddasai. Suna iya kai ƙara. 39In kuma akwai wani abu har yanzu da kuke so ku kawo, dole a daidaita shi a majalisa. 40Yadda yake a yanzu, muna a hatsarin amsa zargin ta da hargitsi saboda abin da ya faru yau. Da yake ba za mu iya ba da dalilin da ya sa aka yi wannan hargitsi ba.” 41Bayan da ya faɗi haka, sai ya sallami taron.

Copyright information for HauSRK